✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta tashi gari guda a Jigawa

Kusan ilahirin garin yanzu ambaliyar ta lalata

Wani mamakon ruwan sama da aka tafka ya yi sanadin raba daruruwan mutanen kauyen Karnaya da ke Jihar Jigawa da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa.

Aminiya ta gano cewa ambaliyar ta kuma lalata fiye da rabin gidajen da ke kauyen.

Kauyen na Karnaya dai na dab da Dutse, babban birnin jihar.

Ambaliyar dai wacce aka fara tun misalin karfe 6:00 na yammacin Asabar ta tayar da mazauna kauyen tsaye har zuwa yammacin Lahadi, inda suka koma neman mafaka a azuzuwan makarantar yankin.

Da yake zantawa da Aminiya, daya daga cikin mazauna kauyen, Ado Karnaya, ya ce, “Tun jiya har yanzu ban samu na ci abinci ko kuma na rintsa ba. Idonmu biyu muna kokarin tallafa wa ’yan uwanmu.”

Da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Yusuf Sani Babura, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ambaliyar ta tashi kusan ilahirin garin, yayin da su kuma suke kokarin samar da matsugunai da abinci ga mutanen da lamarin ya shafa.

“Gaskiya ne ilahirin kauyen ruwa ya tafi da shi. Yanzu haka ina wajen tare da ma’aikatana muna kokarin ba su tallafin abinci da muhalli.