Ambaliyar ruwa a garin Bajoga, hedkwatar karamar hukumar Funakaye a jihar Gombe, ta yi ajalin wani karamin yaro tare da rusa gidaje da dama.
An sami ambaliyar ce sakamkon ruwan da aka tafka kamar da bakin kwarya a yankin.
- An dawo da dokar hana hawa babur da daddare a Katsina
- Ta’addanci: Daruruwan mutane sun tsere daga yankin Birnin-Gwari
Tuni dai Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya umurci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) da Ma’aikatar Muhalli da su je su samu cikakken bayanin yadda za a tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa don a rage musu radadi.
Gwamnan ya kuma aike da sako jajen ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnatin Jihar, Ismaila Uba Misilli.
Sanarwar ta kuma ce Gwamna Yahaya ya ce gwamnatinsa ta himmatu sosai wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar, yana mai cewa za su tallaf musu.
Daga nan sai ya shawarci jama’a da su dauki gargadin da hukumomi ke yi na yiwuwar samun ambaliya, kuma su nesanci wuraren da ke fuskantar barazanar a matsayin mataki na rigakafi.