Sama da mutum miliyan 200 ne ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassan kasashen Bangladesh da Indiya bayan tafka mamakon ruwan sama.
Bayanai daga kasashen biyu sun tabbatar da cewa ambaliyar ta kuma yi ajalin mutum 57.
- An gano nau’in sauron da ba ya jin maganin Maleriya a Jigawa
- Dan takarar da ke hannun ’yan bindiga ya lashe zaben fid da gwanin PDP a Kaduna
Rahotanni sun ce, kimanin mutum miliyan daya ne ambaliyar ta shafa a yankin Arewa maso Gabashin Bangladesh.
Wannan ba shi ne karon farko da wannan yankin ya yi fama da irin wannan mummunar ambaliyar ba.
A kasar Indiya kuwa, kimanin kauyuka 100 ne ambaliyar ta mamaye a Zakiganj kamar yadda wani jami’in gwamnati a yankin, Mosharraf Hossain ya bayyana.
A cewar jami’in, “Kawo yanzu kimanin mutum miliyan 200 ne ambaliyar ta jefa cikin mawuyacin hali, kana mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya a wannan makon sakamakon ambaliyar.”
Masana sun ce sakamakon sauyin yanayin da ake fuskanta, sassa da dama daga Bangladesh da wasu makwabtansu a Indiya na fuskantar hadarin fama da ambaliya.