Akalla mutum 400 ne suka rasa rayukansu a sandiyyar ambaliyar ruwa da ta auku a gabar tekun Gabashin Afirka ta Kudu a ranar Talata.
Yanzu haka dai ana ci gaba da aikin ceto wanda lamarin ya rutsa da su.
- An kama masu zanga-zanga kan yunkurin kone Alkur’ani a Sweden
- NAJERIYA A YAU: Abin da Ya Sa Aka Yafe wa Dariye Da Jolly Nyame
Rahotanni sun ce daga ciki adadin wadanda suka mutun har da ma’aikatan agaji.
Firaministan lardin KwaZulu-Natal, Sihle Zikalala, yayin wata zantawa da manema labarai ya kara da cewa wasu mutum 63 har yanzu ba a gano inda suke ba.
Daya daga cikin masu aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, ya fuskanci matsalar sarkewar numfashi wanda sai daukar shi a aka yi cikin gaggawa zuwa asibiti, daga bisani kuma rai ya yi halinsa.
Ruwan saman ya fara barkewa a yankin Gabashin kasar ne da ambaliyar ruwa ya yi kamari, lamarin da ya ba da damar gudanar da bincike da ayyukan agaji bayan da wata guguwa ta ta’azzara lamarin.
Ambaliyar ta mamaye wasu sassan birnin Durban da ke gabar tekun Kudu maso Gabashin kasar a farkon makon da ya gabata tare da kashe hanyoyi da lalata asibitoci da kuma lakume gidaje da dama.