Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta tabbatar da mutuwar mutum 40 yayin dai dubbai kuma suka rasa muhallai da gonakinsu sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan da ta fadawa jihar a ‘yan kwanakin nan.
Babban sakataren hukumar, Alhaji Sani Ya’u Babura wanda ya tabbatar da alkaluman ya kuma ce tuni hukumarsa ta kammala duk shirye-shiryen da suka kamata domin aikewa da kayan tallafi ga wadanda abin ya shafa.
- Ambaliyar ruwa ta ci rabin gari, ta kashe mutum 5 a Jigawa
- Ambaliya: Sama da mutum 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi
Bugu da kari, Alhaji Sani Ya’u Babura ya ce hukumar za kuma ta nemi karin tallafi daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).
A wani labarin kuma, Kungiyar Ci Gaban Masarautar Hadeja (HEDA) ta alakanta matsalar ambaliyar da ake samu duk shekara kan gazawar gwamnatocin baya a jiha da ma tarayya wajen kin yin katabus don dakile ta.
Masarautar Hadeja dai wacce take karkashin mazabar dan Majalisar Dattijai ta Arewa maso Gabashin Jigawa na da kananan hukumomi guda takwas da suka hada da Hadejia, da Kaugama, da Auyo, da Malammadori, da Birniwa, da Gurin, da Kirikasanma da kuma Kafin Hausa.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Sarki Kafinta wanda ya yi jawabi ga ‘yan jarida a garin ya bayyana takaicinsa matuka kan irin halin ha’ula’in da jama’a da dama suka tsinci kansu a yankin masarautar saboda ifitla’in.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafawa yankin da nau’o’in iraruwan shuka daban-daban da kuma ‘ya’yan kifaye da za a zuba a kududdufansu bayan ambaliyar.
Da yake mayar da martani, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da ambaliyar ta Hadeja a jihar Jigawan wacce ta janyo asarar rayuka da ma dimbin dukiyoyi, yana mai bayyana ta a matsayin babbar barazana.