Mamakon ruwa da aka yi ranar Alhamis bayan wani ruwan sama a Jihar Bauchi ya jawo ambaliyar ruwa, inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.
Hukumomi a Jihar sun bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a sanadiyyar ambaliyar ruwan ya karu zuwa mutum 13 a ranar Juma’a.
Alkaluman da aka fitar a farko sun nuna mutum biyar ne suka rasa rayukansu a Karamar Hukumar Jama’are sakamakon ambaliyar ruwa, sai mutum 24 da suka samu raunuka a kananan hukumomi 18 na jihar.
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA) ta ce, a Karamar Hukumar Jama’are mutum biyar ne suka rasu, mutum uku a Karamar Hukumar Gamawa, sai mutum uku a Ningi, mutum daya a Toro da kuma mutum daya a Darazo.
Hukumar ta SEMA ta ce, ambaliyar ruwan ta shafe gidaje sama da 1,600 da kuma gonaki sama da 5,000 da ruwan ya shafe amfanin gonarsu.
Ambaliyar ruwa tuni ta fara barazana ga wasu jihohi a Najeriya, tun bayan da daminar bana ta kankama.