Akalla gawarwakin mutum 15 ne aka tsinta a kogin Ngadabul da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno bayan wami mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) na shiyyar Arewa maso Gabas, Muhammad Usman, ne ya tabbatar da alkaluman a ranar Laraba a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri.
- Yadda ambaliyar ruwa ta durkusar da kasuwanci a Kantin Kwari
- Jam’iyyarmu na da masu zabe miliyan 22 – LP
Usman ya ce, mutanen da suka nitse a kogin wadanda ke gabarsa ne kuma adadin zai iya karuwa.
Ya kuma gargadi iyaye da masu kula da su da su fadakar da ‘ya’yansu ke zuwa yin ninkaya a cikin kogin don guje wa nitsewa a ciki.
Usman ya kuma ce ambaliyar ruwa a yankin Arewa maso Gabas na da matukar tayar da hankali.
“NEMA a matsayinta na hukumar ba da agaji ta tsunduma aikin wayar da kan jama’a kan illolin ambaliya da matakan kariya daga ita.
“Muna ta ganawa da masu ruwa da tsaki daban-daban kan wayar da kan jama’a da kuma samar da kayan agaji ga al’ummomin da abin ya shafa,” inji Usman.
A halin da ake ciki kuma, tuni rundunar tsaron farin kaya ta sibil defens (NSCDC) reshen Jihar Borno ta tura jami’anta gabar kogin domin fatattakar yaran da ke shirin shiga ciki da nufin yin ninkaya.