Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwan sama ta yi wa barna a Jihar Jigawa.
Ya umarci Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) da sauran hukumomin tallafi da su tantance irin asarar da ambaliyar ta haifar da nufin agaza wa wadanda abun ya shafa da kayan bukatu cikin gaggawa.
“Shugaban Kasa zai rika bibiyar rahotannin ambaliya a fadin kasa domin ganin hukumomin da hakkin ke kansu na cikin kyakkyawan shiri da kuma kai dauki a wurin da aka samu iftila’i da kuma dakile barazanar aukuwar iftil’ai”, inji sanarwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar.
Shugaban ya yi jaje ga iyalai da dangogin wadanda suka yi asarar rayuka da gidaje da gonaki da sauran dukiyoyi a ambaliyar da aka samu a sassan jihar ta Jigawa.
- Soja ya bude wa karamin yaro wuta a Borno
- Likitoci za su tsunduma yajin aiki.
- Yadda ambaliya ke barazanar kawo yunwa a Najeriya
Ya yaba da abin da ya kira saurin daukar mataki da gwamnatin jihar ta yi bayar faruwar iftila’in.
A baya-bayan nan yawaitar ambaliyar na haifar da damuwa musamman ganin yadda ta yi sanadin asarar amfanin gona na biliyoyin Naira.
Wasu manoma da abin ya shafa da suka ce sun karbi rancen banki ne domin yin noma a bana sun nun shakku game da yiwuwar su iya biyan basukan.
Manoma da masana a harkar noma na ganin lamarin asarar amfanin gona da aka yi na iya haifar da karancin abinci musamman shinkafa a wannan shekarar.
Tuni dai rahotanni suka nuna farashin kayan abinci, musamman hatsi ke ta hauhawa a kasuwanni.
Shugaban Buhari ya bayyana damuwa game da hauhawar farashin wanda ya ce gwamnatinsa na kokarin daukar matakan da suka dace domin yi wa tufkar hanci.