✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar gabar teku ta kashe masu yawon shakatawa 3 a Afirka ta Kudu

Karin wasu mutum 17 kuma suna cikin mawuyacin hali

Wata ambaliyar teku ta yi ajalin mutum uku, ta jikkata wasu kimanin mutum 17  a gabar teku ta Bay of Plenty da ke birnin Durban na Afirka ta Kudu, suna tsaka da shakatawa.

Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar KwaZulu-Natal, ya ce ambaliyar tekun ta auku ranar Asabar.

Ya kuma ce kawo yanzu, mutum 17 ne suka jikkata, kuma yanzu suke can a cikin mawuyacin hali.

Lamarin ya auku ne wajen misalin karfe 5:00 na yammaci a agogon kasar, kimanin karfe 4:00 na yamma a agogon Najeriya da Nijar, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin garin eThekwini ta tabbatar.

Ofishin ya kuma ce yanzu haka ma’aikatan ceto 35 ne suke ta kokarin kai agaji, yayin da ma’aikatan lafiya sun duba sama da mutum 100 a wajen.

Daga cikin wadanda suka mutu har da wani yaro mai kanana shekaru.

Iftila’in na zuwa ne bayan wata mummunar ambaliyar ruwan da ta tilasta rufe bakunan teku a birinin, wacce aka yi a watan Afrilu.

Ambaliyar dai ta halaka sama da mutum 400. Bugu da kari, bakunan tekun na birnin Durban na shirin karbar dubban masu ziyara saboda lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.