Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da rasuwar mutane biyu a yayin da wasu biyu suka bace a sanadiyyar wani ruwan sama da aka yi a ranar Talata wanda ya haifar da ambaliya a sassan birnin Ibadan, fadar jihar Oyo.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kodineto na Hukumar NEMA shiyyar Kudu maso Yamma, Olanrewaju Kadiri, ya ce ambaliyar ruwan ta yi sanadin rushewar wasu gidaje da shaguna da kadarori na miliyoyin kudi.
Ya ce yanzu haka hukumar da hadin kan SEMA ta Jihar Oyo da ƙungiyar Red Cross suna kan aikin ziyarar unguwannin da lamarin ya shafa domin kididdige irin barnar da ambaliyar ta haifar.
A binciken Aminiya ta gano cewa ambaliyar ta shafi yankin Karamar Hukumar Ibadan ta Yamma ne inda al’amuran yau da kullum suka tsaya cik na tsawon awoyi biyar da aka yi ana yin ruwan saman kamar da bakin ƙwarya.
- Hajjin 2025: Kafin alƙalamin N8.5 maniyyata za su biya a Legas
- Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ba ta hannunmu —Hisbah
Binciken ya nuna cewa matakin hana zuba shara a magudanun ruwa da suka kewaye birnin Ibadan da gwamnatin jihar ta dauka tun kafin isowar wannan lokaci ya taimaka wajen samun saukin ambaliyar.