Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da gawa akalla 500 daga makabarta a garin Mariga da ke Jihar Neja.
Babban Limamin Mariga, Alhaji Alhassan Na’ibi, ya ce dole ta sa sai da suka sauya wa wasu gawarwaki kimanin 100 da aka binne a makabartar wuri zuwa wata makabarta ta daban.
- DAGA LARABA: Tashin Hankalin Da Samari Ke Ciki Amma Suke Boyewa
- Girman kai: Shawarwari ga matasa
- An banka wa barayin waya wuta a Delta
Babban limamin ya ce zuwa ranar Talata da dare, “Muna neman gawa akalla 500 da aka binne a Makabartar Mariga da ruwa ya tafi da su.”
Ya ci gaba da cewa al’ummar garin sun shiga tashin hankali bisa yadda ambaliya ke hako gawarwaki daga cikin kabari tana tafiya da su.
A cewarsa, a tsawon shekara 60 irin haka ba ta taba faruwa a makabartar ba.
Ya danganta girman ambaliyar da ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kusa da makabartar.
Don haka ya roki Gwamnatin Jihar Neja da ta gaggauta kawo musu dauki game da wannan matsala domin magance ta gaba daya.