Amurka ta bada umarnin ficewa daga unguwar Montecity da ke California, inda Yariman Ingila Harry da fitattun masu gabatar da shirin talabijin, Oprah Winfrey da Ellen Degenres, da kuma taurarin finafinai Jennifer Aniston, da Adam Levine, da Rob Lowe ke zaune saboda mummunar ambaliya.
Hukumar agajin gaggawa ta lardin Santa Barbara ce ta bada umarnin kwashe mutanen unguwar, wadanda da yawancinsu fitattun mutane ne da manyan masu kudi, bayan ambaliyar ta shafe yankin.
- Ganduje zai tantance jam’iyyu kafin kamfe a filin wasa na Sani Abacha
- APC ta fi PDP shiga matsala —Kofa
A wasu sassan yankin dai, gwamnati ta bai wa kusan mazauna 32,000 umarnin kaura daga gundumar ta Santa Cruz, tare da rufe da dama daga hanyoyi.
A hannu guda Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya dokar kar ta kwana a daukacin Jihar California, bayan ambaliyar ta hallaka akalla mutane 12.
Sanarwa da Biden ya fitar ranar Litinin ta ce hakan zai taimaka wa Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasar shawo kan lamarin, da kuma bai wa wadanda abin ya rista da su agajin da ya kamata.