Akalla yara biyu sun rasu, wani mutum daya kuma ya bata bayan shafe kwana biyu ana tafka mamakon ruwan sama a Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Kamfanin Dillancin Labarun Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ruwan saman ya kuma lalata gidaje da gonaki da dama.
Shugaban Karamar HJukumar, Alhaji Wada Faka ya ce yara biyun sun rasa ransu ne bayan gini ya fado musu a ka lokacin da ake tafka ruwa, yayin da wasu kuma suka samu raunuka da dama.
Ya ce daya daga cikin yaran mai kimanin shekaru 10 ya rasu bayan gini ya danne shi a kauyen Kiyako, sai kuma dayan mai kimanin shekaru bakwai shi ma a kauyen Masaya duk dai a karamar hukumar.
Alhaji Wada ya yi bayanin cewa ambaliyar ta yi sanadiyyar shafewar dubban gonaki da kuma tafiyar dabbobi da dama.
Kazalika, ya ce tun safiyar Litinin din aka aka nemi wani mutum mai kimanin shekaru 40 a kauyen Samamiya amma ba a ji duriyarshi ba har zuwa yau.
Sauran garuruwan da rahotanni suka nuna ambaliyar ta yi wa barna sun hada da Malamawar Gangaran, Babaldu, Wurno, Kiyako da kuma Samamiya
“Maganar da nake yi da kai yanzu haka mun tura jami’anmu zuwa wadannan kauyukan don kiyasta irin barnar da ambaliyar ta yi domin tallafa musu.
“Mun kuma tura bayanai zuwa hukumar Agajin Gaggawa ta Jigawa don ita ma ta tallafa musu.
“Na sami babban sakataren hukumar ya kuma yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa”, inji shugaban.
Idan za a iya tunawa, a ranar 19 ga watan Agusta sai da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta shirya taron masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a a Dutse a kan barazanar ambaliyar a bana.