✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya ta kashe mutum 37 a Adamawa

Mutum 171,000 sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a Jihar Adamawa.

Mutum 37 sun rasu, wasu 171,000 kuma sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a sassan Jihar Adamawa.

Babban Sakataren Hukumar Agaji ta jihar, Dokta Muhammad Sulaiman, ya ce mutum 58 sun samu raunuka sannan ruwan ya shanye gonaki masu fadin kadada 89,000.

Suleiman ya ce girman ambaliyar ya wuce yadda aka yi hasashe kuma ya gurgunta harkokin kasuwanci da rayuwar jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa wuraren da ambaliyar ta lalata sun hada da makarantu da asibitoci da wuraren ibada da gine-ginen jama’a.

Ya kara da cewa hukumar ta raba kayan tallafi a sansanoni 10 da aka tsugunar da mutanen da ambaliyar ta shafa a sassan jihar.