✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta kashe mutum 24 a Jigawa

Abin ya rutsa da gidaje 3,000 a Karamar Hukumar Gwaram, inji wani mazauni

Mutum 24 sun mutu baya ga asarar dukiyoyi sakamakon ambaliya a 17 daga cikin Kananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa.

Hukumar Agaji ta Jihar Jigawa (SEMA) ta ce an tsugunar da mutanen da ambaliyar ta yi wa barna a makarantu yayin da wasunsu suka koma da zama a wurin ’yan uwansu.

Babban Sakataren Hukumar, Yusuf Sani Babura ya ce ambaliyar ta share gidaje 50, amma wani wanda abun ya shafa a garin Maruta na Karamar Hukumar Gwaram ya ce sama da gidaje 3,000 sun rushe.

Sakamakon haka an mayar da mutanen da iftila’in ya shafa a Gwaram zuwa sansanin ’yan gudun hijira, inda rahotanni ke cewa wata mata ta haihu a nan.

Wasu Kananan Hukumomin da ambaliyar ta shafa a Jihar Jigawa sun hada da Birnin Kudu, Babura, Malam Madori, Jahun, Ringim da Kirikasanma.

Mutum hudu sun mutu a Birnin Kudu, uku a Ringim da wasu ukun a Malam Madori.

Ba a samu asarar rai ba a Jahun da Kirikasamma, sai dai ambaliyar ta katse wasu kauyuka gaba dayansu.

Sani Babura ya ce gwamnatin jihar ta sayo jiragen ruwa guda 40 domin al’ummomin da ambaliyar ta shafa, wanda daga ciki ta SEMA ta riga ta raba guda 10.

Ya ce tuni hukumar ta fara rabon abinci da magunguna da sauran kayan tallafi ga wadanda suka yi asara ambaliyar.