Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 195 tare da shafar rayuwar wasu 322,000, a Jamhuriyar Nijar.
Hukumomin kasar sun ce 59 daga cikin mamatan ruwa ne ya ci su, 136 kuma faduwar gini a kansu ne ya kashe su, sannan wasu sun samu raunuka.
- UAE ta dakatar da ba ’yan Najeriya bizar zuwa Dubai
- Pakistan: An haramta wa Imran Khan tsayawa takara
Hukumar Kare Al’umma ta Jamhuriyyar Nijar ta bayyana cewa ambaliyar da aka samu a daminar bana na cikin mafiya muni a tarihin kasar.
A farkon watan Oktoba da muke ciki hukumar ta sanar cewa ambaliya a daminar bana ta yi ajalin mutum 192 tare da shafar rayuwar wasu dubu 263 a kasar.