Matafiya da direbobi sun shiga cikin tsaka wuya a Sabon Garin Kwami da ke Jihar Gombe, bayan ruwan sama ya sake rushe gadar wucin gadi ta Oji, wadda ta daɗe da lalacewam
Ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama mai karfi da ya haddasa cunkoso da tsaikon zirga-zirga na tsawon sa’o’i uku.
- Hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 22.22 a watan Yuni — NBS
- Rashin shugabanci na gari ya sa ilimi taɓarɓarewa a Yobe — ADC
Lamarin ya nuna halin da wannan gada da ta shafe kusan shekaru 20 tana cikin mummunan yanayi ba tare da gyara ba.
Gadar Oji na da matuƙar muhimmanci wajen haɗa Gombe da sauran yankuna kamar su Dukku, Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Abuja, Taraba da kuma Adamawa.
Amma al’ummar yankin na ƙorafin cewa gwamnati ta kasa ɗaukar matakin gyara ta duk da muhimmancin ta.
Nasiru Abubakar Kwali, wani direban motar haya ya bayyana cewa: “Mun kwashe sa’o’i uku a nan a ranar Laraba saboda ruwa ya rushe gadar. Wannan matsalar ta daɗe tana barazana ga rayukanmu, amma gwamnati ta yi hiru.”
Saboda lalacewar gadar, matafiya da dama sun sauka daga motoci suna tafiya a ƙafa domin samun hanyar da za su ci gaba da tafiya.
A wasu lokuta, ana samu rahotannin haɗura sakamakon lalacewar hanyar.
Wasu mazauna yankin sun zargi gwamnati da yin watsi da su.
“Da hanya ce da ke kai wa gidan wani babban ɗan siyasa, da an riga an gina gada tun tuni,” in ji wani fasinja.
Yanzu haka, jama’a na roƙon gwamnatin jihar da ta tarayya da su gaggauta ɗaukar matakin gyara gadar kafin lamarin ya ƙara tsananta.
“Wannan batu ba na siyasa ba ne. Rayukanmu ne ke cikin hatsari,” in ji Nasiru.
Yayin da damina ke ƙara sauka, fargaba na ƙaruwa cewa gadar na iya haddasa mummunan yanayi idan ba a ɗauki matakin da ya dace.