✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya ta kara tasar wani kauye a Jigawa

Ambaliyar ruwa ta shanye garin Gamayin da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa a Jihar Jigawa.

Ambaliyar ruwa ta shanye garin Gamayin da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa a Jihar Jigawa.

Mai magana da yawun al’ummar Gamayin, Malam Ibrahim Musa Gamayin, ya shaida wa Aminia cewa ambaliyar ta lalata gidaje da dama, tare da raba mutane da muhallansu.

Sai dai ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, sai dai ta dukiyar miliyoyin Naira da kuma amfanin gona da ruwan ya yi awon gaba da su.

Malam Ibrahim ya ce a halin yanzu yawancin mutanen garin suna tsugune ne a wasu gine-gine da ke kan tudu da ruwan bai riga ya shanye ba a garin.

Don haka ya yi roko ga Gwamnatin Jihar Jigawa da ta kawo musu dauki domin a halin yanzu suna cikin mawuyacin hali.

Da yake jawabi kan lamarin, Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namaddi, ya jajanta musu tare da ba da tabbacin kawo musu kayan agaji daga gwamnatin jihar.