Ambaliyar Ruwa a Jihar Kano, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31 tare da lalata gidaje 5,280 a ƙananan hukumomi 21 a jihar.
Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Isyaku Kubarachi ne, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi mutum 31,818 tare da lalata gidaje 5,280.
Kazalika, gonaki 2,518 da ke da faɗin kadada 976 sun lalace, sannan mutum 31 sun rasa rayukansu.
Kubarachi, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka fuskanta a jihar.
Amma ya ce da yawan gidajen da suka lalace an gina su ne a kan hanyar ruwa.
“Yawancin gidajen da suka lalace na ƙasa ne kuma an gina su a hanyar wucewar ruwa. Mutane suna barci ba tare da tunanin gidajensu za su rushe ba, amma ruwan sama mai ƙarfi ya haifar da ambaliya” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a baya an yi hasashen ambaliyar za ta shafi ƙananan hukumomi 14 ne kaɗai , amma a yanzu ta shafi 21 ciki har da Wudil, Gwale, Nassarawa, Dala, Tarauni, Dawakin-Tofa, Dambatta, da sauransu.
Kubarachi, ya ce hukumar ta gabatar da wani shiri ga gwamnatin jihar don samar da kayan tallafi ga magidantam da lamarin ya shafa.
Ya kuma jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki matakan kariya kafin saukar damina don kare rayuka da dukiyoyi.
“Gwamnatin jiha na aiki don samar da tallafi ga dukkanin ƙananan hukumomi 21 da ambaliyar ta shafa, kuma muna fatan samun sakamako mai kyau nan ba da jimawa ba. A halin yanzu, wadanda lamarin ya shafa suna zaune tare da maƙwabtansu da ‘yan uwansu,” in ji Kubarachi.