✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Masarautar Kaltungo ta bai wa Borno tallafin kayayyaki

Shehun Borno, ya yaba da tallafin kayayyakin a madadin masarautar.

Mai Martaba Sarkin Kaltungo kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna na Jihar Gombe, Injiniya Saleh Muhammad Umar ya miƙa kayan tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.

Sarkin ya miƙa kayan tallafin ne ga Mai Martaba Shehun Borno, Dokta Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, a madadin masarautar Kaltungo.

Tallafin wani shiri ne na rage wa waɗanda ambaliyar radadin wahalar da suka tsinci kansu.

Kayan tallafin sun haɗa da barguna 182 da turamen atamfa 156 da shadda 50 da audugar yara guda 5,200 ds kofuna 60 da butoci 24 da rariya 24 da botiki 24 da tukwane guda 20.

Sauran kayan sun haɗa da murhu mara hayaƙi da turame da tabaɓre da buhunan hatsi bakwai da zannuwan  gado da sauransu.

Shehun Borno ya gode wa Sarkin kan tallafa wa al’ummar jihar da suka tsinci kansu a tsaka mai wuya sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwan da ta same su.

Ya kuma bayyana cewa tallafin zai taimaka matuƙa ga jama’ar Masarautar Borno.

Shehun Borno ya kuma yi addu’ar samun haɗin kai tsakanin masarautun biyu.