Kwamitin Kula da Aukuwar Bala’o’i da Fadakarwa kan annoba na Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ya shawarci gwamnatocin Najeriya a dukkan matakai, da su daura damarar dakile barkewar annoba dalilin ambaliyar ruwa da aka samu a kasar.
Shugaban Kwamitin, Dokta Abubakar Hassan ne ya sanar da hakan a Lokoja, babban birnin Kogi a ranar Litinin
- Buhari ya sauka a London domin ganin likita
- An fara yi wa baki binciken kwakwaf kafin shiga harabar Majalisa
Kwamitin ya roki gwamnatocin da su yi kokarin samar da tsaftataccen ruwan sha ga kauyukan da ambaliyar ta shafa, kasancewar hanyoyin samar da ruwan yankunan sun gurbace.
Sanarwar ta kuma yaba da kokarin Gwamnatin Tarayya na samar da na’urar tace ruwan sha a kasar, tare da kiran a sanya yankunan da aka samu ambaliyar cikin wadanda za a samawa na’urar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta kara kulawa da kauyukan da abin ya shafa, tare da rabon gidajen sauro, domin dakile cizon kwari, musamman Sauro da Kudajen Tsandu da ke sanya cutar bacci.