Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta ce ta fara rarraba kayayyakin tallafi ga manoma 35,000 da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar a shekarar 2020.
Shugaban hukumar, Alhaji Yusuf Sani ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Talata a Dutse cewa kayan ragowar wadanda Gwamnatin Tarayya ta tallafawa da jihar ne bayan ambaliyar 2018.
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 40 a Jigawa
- Duk wanda ya saki matarsa ko da a shirin fim ne ta saku — Dokta Bashir
Ya ce, “Mun roki Gwamnatin Tarayya ta bamu ragowar kayan don mu yi amfani da su kuma ta amince, yanzu haka mun fara rabon ga Kananan Hukumomi 20 da ambaliyar ta shafa a 2020.
“Mun fara da Malam Madori, kuma za mu ci gaba zuwa sauran Kananan Hukumar19, har sai dukkan manoman da iftila’in ya shafa sun ci gajiyar tallafin,” inji shugaban.
Ya kara da cewa sama da manoma 3,500 ne suka amfana da tallafin a Karamar Hukumar ta Malam Madori.
Kayan tallafin da aka raba sun hada da hatsi (ridi, shinkafa, gero da dawa), maganin feshi da magunguna kwari.
Rabon kayan tallafin dai ya biyo bayan gwajin girman asarar da manoman suka tafka sakamakon ambaliyar.
Daga nan sai ya shawarci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata domin su farfado daga asarar da suka yi.