✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dage auren amaryar da ta bata gab da bikinta

An dage bikin bayan a tsinci amaryar a kan titi ba ta iya magana.

Wanzu haka amaryar nan da ta yi batan dabo kwana biyu kafin aurenta a Kano ta dawo inda ta hadu da iyayenta a safiyar Talata.

Kawun amaryar, Gwani Yahuza  Gwani Danzarga ya shaida wa Aminiya cewa wani mutum ne ya kira mahaifiyarta ya gaya mata cewa sun tsinci wata yarinya a kan Titin Jami’ar Bayero.

“Ana sanar da mu cewa an ga wata yarinya a kan titin Jami’ar Bayero sai muka hanazarta zuwa wurin inda muka samu Amina tana zaune tana ta kuka,” inji shi.

A cewar Gwani Yahuza, duk da cewar sun samu ’yar tasu a wani hali na rashin magana, amma sun gode wa Allah da ganin ta da suka yi cikin koshin lafiya.

Ya ce a lokacin, “Ba ta iya magana sai dai ta yi nuni da hannunta, amma mun godewa Allah da yadda muka same ta Alhamdulillah.”

Wata majiya a iyalan amarya Aminya ta bayyana cewa an dage gudanar da bikin amaryar har zuwa lokacin da za ta kara murmurewa.

Tun a ranar Juma’a iyayen amarya Amina Gwani Danzarga suka bayayana labarin bacewarta a yayin da take dawowa daga unguwar Dorayi inda ta je ta kai wa wata kawarta katin jarrabawarta.