Ajali idan ya yi kira ko babu ciwo sai an tafi, a yayin da mai yankan kauna ta cimma wani sabon ango mai suna Jamilu Abdulhamid, bayan kwana biyu da angwancewa da amaryarsa mai suna Saratu Salisu.
Jamilu ya riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi tare da amaryarsa a kan hanyarsu ta zuwa Abuja bayan tasowa daga Kano.
- Dalilin da APC ta fadi zaben wasu jihohi a 2019 —Buhari
- Yadda ake bikin rufe Gasar Rubutattun Wakokin Hausa a Sakkwato
Aminiya ta samu cewa an daura auren Saratu da Jamilu a ranar Lahadin da ta gabata, a unguwar Goron Dutse da ke birnin Kano.
Bayan shagalin bikin ne suka kama hanyar zuwa Abuja da zummar cin amarcinsu a can, kafin daga bisani su wuce garin Benin na Jihar Edo, inda a nan za su kafa tubalin shiga sabuwar rayuwa a matsayin mata da miji.
A zantawarsa da Aminiya, wani dan uwan amaryar mai suna Abdulrazaq Salisu Abdul ya ce dukkanin ’yan uwa da abokanan arziki suna cike da damuwa dangane da wannan rashi na ba-zata.
“Muna cikin damuwa, duk lokacin da ta farka daga doguwar sumar da ta yi sakamakon buguwa da ta samu a hatsarin, mijinta take fara tambaya, duk abin da muka fada mata ba ta yarda.
“Da farko mun sanar da ita cewar an dauke shi zuwa wani asibitin amma ta ci gaba da tambaya.
“Mun rungumi wannan lamari a matsayin kaddara daga Allah, sai dai tabbas wannan mutuwa za ta girgiza Saratu da zarar da warware,” a cewarsa.
Ma’auratan sun gamu da mummunan tsautsayin ne a ranar Talata, a daidai garin Rijana da ke Jihar Kaduna.
Bayanai sun ce nan take Jamilu ya rasa ransa, ita kuma amaryar aka garzaya da ita zuwa asibitin Doka da ke garin na Rijana kafin daga bisani a mayar da ita zuwa Asibitin Barau Dikko da ke cikin birnin Kaduna.
Shi ma wani dan uwan mamacin mai suna Idris Abdulhamid, ya ce jim kadan kafin rasuwar yayan nasa sun yi waya.
“Yayana da amaryarsa sun tsaya a Kaduna sun yi sallah sannan suka ci abinci.
“Na bar Kano ranar Litinin da zummar za mu hadu a Abuja, kafin daga bisani mu wuce garin Benin, babban birnin Jihar Edo.
“Na halarci bikin, suna matukar kaunar junansu, tabbas mun yi babban rashi,” a cewar Abdulhamid.
’Yan uwa da abokan arziki na ci gaba da nuna alhininsu game da rasuwar sabon angon.