Wata sabuwar amarya ta daba wa angonta wuka ta aika shi lahira, kwana biyu bayan daurin aurensu a Jihar Adamawa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, ta tabbatar da faruwa lamarin a kauyen Wuro Yanka da ke Karamar Hukumar Shelleng ta Jihar.
- Gwamnatin Filato ta janye dokar hana tuka Keke NAPEP
- Jami’in gwamnati ‘ya kashe kansa’ bayan EFCC ta gayyace shi
“Matashiyar ta bukaci mijin nata da ya rasu ya sake ta cikin ruwan sanyi sabobda ba ta son auren dolen da aka yi mata da shi, amma ya ki.
“Bayan ta yi ta neman ya sake ta shi kuma yana ki, sai ta fusata, ta dauki wuka ta daba masa a ciki; An garzaya da shi asibiti inda likitoci suka tabbatar cewa ya rasu,” a cewar majiyar Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).
An cafke amaryata bayan ta kashe ango
Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce, “An cafke matar da ake zargin ne a ranar Litinin kan kashe mijinta, mai shekara 35 bayan ta nemi ya sake ta ya ki.
“Kawo yanzu, bincike ya nuna cewa wadda ake zargin an yi mata auren dole ne da mijin nata a ranar 6 ga watan Agusta,” inji Nguroje a ranar Laraba a Yola.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamwa, Aliyu Alhaji, “Ya sa a binciki lamarin cikin tsanaki tare da gaggauta gurfanar da matar a gaban kotu domin ya zama izina ga sauran mutane,” inji shi.
Babu auren dole a Musulunci
Da ya ke zantawa da NAN kan lamarin, wani malamin addinin Musulunci a Yole, Ustaz Abdullah Hamman, ya ce auren dole ba shi da gurbi a Musulunci.
“Musulunci ya ba wa iyaye damar zaba wa ’ya’yansu gida nagari da za su yi aure amma bai ce a yi auren dole ba,“ inji malamin.
Ya jaddada bukatar iyaye su daina yi wa ’ya’yansu auren dole saboda yana haifar da illa mai gairma a cikin al’umma.