✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amarya da ango da wasu mutum 40 sun kwanta bayan cin abincin biki a Afghanistan

Yanzu haka dai an fara bincike kan musabbabin matsalar

Akalla mutum 42, ciki har da ango da amarya, sun kwanta rashin lafiya a a Afghanistan bayan cin abincin biki, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka tabbatar ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne a lardin Takhar da ke Arewacin kasar ranar Lahadi.

Mubin Sufi, wani jami’i a ofishin ’yan sanda na lardin ya ce lamarin ya faru ne yayin bikin a kauyen Takhar Abad da ke gundumar Chah Hab da daren Lahadi.

Ya kara da cewa an garzaya da mutanen zuwa wani asibiti, inda suke ci gaba da samun kulawar ma’aikatan lafiya.

Dan sandan ya ce tuni aka cafke mutum uku bayan samun rahoton lamarin yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin matsalar. (Xinhua/NAN)