Wasu ’yan uwan juna uku a Jihar Kwara sun gamu da ajalinsu bayan cin abinci mai dauke da guba.
Lamarin ya afku a Karamar Hukumar Ilorin ta Gabas, yayin da mutanen biyar ’yan gida daya suka ci wata malmala ta ‘amala’.
Bayanai sun ce an garzaya da su Cibiyar Lafiya ta Igboro, inda a nan uku daga cikinsu suka ce ga garinku nan.
Sai dai binciken da likitoci suka gudanar ya gano cewa abincin da suka ci na dauke da guba wanda shi ne silar mutuwar uku daga cikinsu.
Wannan na zuwa kasa da wata daya, inda aka samu irin wannan rahoto na cin abinci mai guba a yankin Baruteen da Kaiama, wanda ya yi ajalin mutum 17.
Ko da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Hukumar Civil Defence, Babawale Zaid Afolabi game da faruwar lamarin, ya ce ba shi da masaniya game sa faruwar hakan.
Amma jami’in hukumar sanya ido kan cututtuka na jihar Kwara (DSNO), Alhaji Muhammad Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sallami mutum biyu da suka tsallake rijiya da baya.
Ya ce, “Bayan mun isa wajen mahaifinsu ya sanar sa mu cewar sun ci ‘Amala’ amma sai uku daga ciki suka fara amai, amma an kai su asibitin kwararru na yara da ke Ilorin.
“A yayin da ake kokarin ceto rayuwarsu, uku daga ciki sun bakunci lahira.
“Mahaifin nasu wanda Manomi ne ya sanar da mu cewar shi ne ya kawo garin da aka tuka amalar, amma ba shi da masaniyar abin da ya faru.
Jami’in hukumar, ya ce ragowar biyun da kwanan su ke gaba suna cikin koshin lafiya.