✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amaechi ya ci gaba da duba aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ci gaba da lura da yadda aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 154, bayan tsaikon da…

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ci gaba da lura da yadda aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 154, bayan tsaikon da aka samu saboda bulllar cutar COVID-19.

Amaechi ya bukaci kamfanin CCECC na kasar China da ke aiwatar da aikin da ya dawo da ma’aikata bakin aiki ya bar fakewa da COVID-19.

Amaechi na rangadin ne tare da Ministan Yada Lbarai Lai Mohammed da kuma shugaban hukumar jiragen kasa, Fidet Okhiria.

Sauran wadanda suke tare da shi su ne shugaban kwamitin amintattun hukumar, Ibrahim Al-Hassan da Babban Sakataren hukumar jiragen ruwa Hassan Bello.

Amaechi sanye da farin wanda tare da sauran ‘yan tawagarsa

Rabon ministan da duba yanayin tafiyar aikin tun a watan Janairu, gabanin bullar cutar, wadda ta tilasta rufe tafiye-tafiye domin rage yaduwarta.

Tawagar ta fara duba aikin ne daga tashar jirgi ta Ebute-Metta zuwa tashar Apapa a Jihar Legas.

Sun duba tashoshin jirgin kasa na Ebute-Metta, Agege, Kajola da Papalanto, domin ganin yanayin aikin.

Yanzu haka kamfanin CCECC ya kammala shinfida layin dogo daga Ibadan zuwa Ebute-Metta a Jihar Legas.

Ya kuma ci gada da shimfida titin jirgi zuwa Apapa domin isa zuwa tashar jiragen ruwa na Apapa da zummar rage cunkoson kaya a babbar tashar jirgin ruwa ta Apapa.