✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Sabo Ibadan sun dauki matakan magance matsalar tsagerun matasa

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru da hadin guiwar Kungiyar Ci Gaban Sabo Ibadan (SIDPA) sun kira taron jama’ar gari, a inda suka amince…

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru da hadin guiwar Kungiyar Ci Gaban Sabo Ibadan (SIDPA) sun kira taron jama’ar gari, a inda suka amince da daukar matakin ba-sani-ba-sabo ga dukkan matasan Hausawa da suke aikata miyagun ayyukan da ke bata sunan ’yan Arewa mazauna garin na Ibadan.

Sarkin Hausawan ya kira taron ne domin tattaunawa a kan yunkurin cin zarafin kungiyar ta SIDPA da wasu matasan Hausawa suka yi a makon jiya. Hanzarta isowar ’yan sanda zuwa harabar ofishin kungiyar tare da jefa hayaki mai sa hawaye da harbin bindiga a iska ne ya tarwatsa matasan tare da kama biyu daga cikinsu kafin kazantar al’amarin.

An gudanar da taron ne a harabar masallacin Juma’a na Unguwar Sabo Ibadan. Manyan malaman addinin Musulunci da dattiwan gari masu fada a ji da hakimai da masu unguwanni suna daga cikin mahalarta taron da aka yi a karkashin shugabancin Sarkin Hausawan. Malamai sun yi wa’azi a kan illar aikata miyagun ayyuka a yayin da dattawan gari da sauran jama’a suka tofa albarkacin bakinsu ne a kan samo mafita dangane da wannan matsala da matasan ke haifarwa da ke bata sunan ’yan Arewa mazauna garin Ibadan.

A karshen taron, an amince da daukar matakin ba-sani-ba-sabo ga dukkan matasan Hausawa da aka samu da aikata miyagun ayyuka na shaye-shayen miyagun kwayoyi da ke kai su ga sace-sace da hulda da manyan barayi da ’yan fashi da makami da suke shiga cikin unguwar suna boyewa.

Mahalarta taron sun yi tsokaci a kan kura-kuran da iyaye maza da mata suke haifarwa ta fannin goyon bayan da suke nunawa ga ’ya’yansu wanda yake karfafa masu ci gaba da aikata miyagun ayyuka. Sun ja kunnen masu zagayawa ta bayan gida suna karbo belin irin wadannan matasa daga wurin da suke tsare a hannun ’yan sanda.

Mafiyawancin shugabanni da suka yi jawabi a wajen taron sun jinjina wa kungiyar SIDPA a kan ayyukan da take yi na kawar da zauna-gari-banza daga cikin jama’a. Shugabannin sun fito fili sun bayyana cewa idan an samu ’ya’yan da suka haifa da aikata miyagun ayyuka to kungiya ta hanzarta mika su ga jami’an tsaro ba tare da tausaya masu ko karbar belinsu ba.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Sarkin Hausawan Ibadan Ahmad Dahiru Zungeru ya nemi dukkan masu hali su taimaka wa kungiyar, wacce ta sadaukar da kanta yin amfani da kudin aljihunsu domin gyara wannan unguwa ta Sabo, mazaunin Hausawan Ibadan. Ya ce yanzu haka akwai takardun fom na daukar matasa aiki a wasu kamfanoni da masana’antu da ya nemi irin wadannan matasa su cike domin daukarsu ayyuka a maimakon zama dirshan da suke yi.