Shugabar Matan Fulani ta Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Kasa, Hajiya Baheejah Mahmood Abdullahi ta ce gwamnatocin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi sun yi watsi da al’ummar Fulani makiyaya a Najeriya wajen samar musu da kayayyakin da za su kyautata rayuwarsu ko inganta rayuwar dabbobinsu.
Hajiya Baheejah Mahmud ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da Aminiya a Bauchi, inda ta ce rayuwar Fulani makiyaya a kullum na shiga cikin mawuyacin hali saboda tsana na ba gaira ba dalili, kuma babu wanda yake tausaya musu illa kowace kabila so take ta yi amfani da Fulani don cimma manufa ta kashin kanta ko da a kan mummunan abu ne. Ta ce kuma magautan Fulanin sun siyasantar da al’amarin Fulani ta hanyar nuna musu kiyayya da ambatarsu masu laifi a Najeriya.
Ta ce Fulani ba masu aikata miyagun laifuffuka ba ne, duk Bafulatanin kirki za a same shi mutum ne mai gaskiya, haziki mai aiki tukuru wanda ba ya da lalaci kuma mai bin dokar kasa kuma yana ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da nama da madara da kwai da kuma fatu.
Shugabar matan ta ce “Yau a duk duniya da wuya a samu wata kabila da ’ya’yanta ba sa aikata wani laifi. Kuma a kullum jami’an tsaro suna kama wadanda ake zargi da laifi; amma an taba jin an kama masu laifin ana fadin cewa ’yan kabila kaza ne suka aikata laifin? Me ya sa sai Fulani ake jingina laifi ga kabilarsu? Wannan ai tsanace a fili.”
Ta ce ya kamata in an kama masu laifi a bi diddigi a ga ta ina ne suka aikata laifin kuma su wane ne suka sanya su aikata wannan laifi, me ya sa su aikata laifin, in an yi haka sai a ga an samu bakin zaren kuma an yi musu adalci.
Shugabar ta ce “Fulani sun fi samun kayayyakin kyautata rayuwa a duk Najeriya lokacin mulkin mallaka fiye da wannan zamani. Ta ce “A lokacin Turawa malaman jami’a sun shaida mana cewa Turawa suna yi wa Fulani burtalin shanu, suna gina musu madatsun ruwa suna kuma samar musu da dajin kiwo da audugar shanu ana kuma yi musu huji da allurar rigakafi. Amma a yau duk wadannan babu. Na karanta an ce yau a Najeriya akwai burtalin shanu da dazuzzukan kiwo kowanne sama da 600 a Arewa da gyara su kawai gwamnati za ta yi. Me ya sa gwamnatin ba za ta yi ba? Ko Fulanin ba sa cikin wadanda suka zabe ta, ko su ba ’yan Najeriya ba ne?”
Baheejah ta ce Fulani ne kawai kabilar da a yau a Najeriya ba sa cin gajiyar kayayyakin more rayuwa na gwamnati kamar lantarki da ruwan sha da asibitoci da hanyoyi da ilimi da kayayyakin kawa duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen gina tattalin arzikin kasar nan.
Ta ce abin kunya ne kin amincewa da shirin gwamnati na gina rugage ga Fulani don gwamnati ta ware kudi har Dalar Amurka biliyan 3.9 don gina tashar jiragen ruwa a Warri kuma ta ware har Dala miliyan 99.6 (kimanin Naira biliyan 35.8) don gina tashar sauke kaya ta kan tudu a garin Ibadan ba wanda ya nuna rashin amincewa, me ya sa za a nuna rashin amincewa kan wanda za a yi wa wadansu ’yan Najeriya?
Ta yi kira ga gwamnatoci su yi adalci ga dukkan ’yan Najeriya a kuma dawo da shirin nan na gina wa Fulani ruga domin warware matsalolin Fulani da kuma kyautata rayuwarsu.
Shugabar ta ce “in aka lura za a ga Bayarbe da Ibo da wadansu kabilu duka sun zo suna kasuwanci a Arewa har can cikin kauyuka ba wanda ke tsangwamarsu; amma me ya sa za a tsangwami Fulani a cikin wasu jihohi nasu? Hakan bai dace ba.”