✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Apapa sun koka kan lalacewar hanyar tashar jirgin ruwa

Al’ummar da ke hada-hada a kan hanyar nan da ta haɗa tashar jiragen ruwa ta Legas da sassan ƙasar nan, wato hanyar Apapa na ci…

Al’ummar da ke hada-hada a kan hanyar nan da ta haɗa tashar jiragen ruwa ta Legas da sassan ƙasar nan, wato hanyar Apapa na ci gaba da kokawa bisa taɓarɓarewar hanyar, wacce suka ce tana da matuƙar mahinmmaci ga ɗaukacin ƙasar amma mahukunta na ci gaba da yi mata riƙon sakainar kashi; abin da ya sanya masu amfani da ita shiga halin ha’ula’i.

Aminiya ta zanta da sarkin Hausawan Marinbich da ke Apapa-Legas, Alhaji Almustafa Abdullahi, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa da yanayin da hanyar Apapa ke ciki. Ya ce baya ga jihohin da ake haƙar man fetur babu wata hanya da ke da matuƙar alfanu tamkar wannan hanya. “Domin duk wani kaya da ake shigowa da shi daga ƙasashen ƙetare a nan ake ɗauka a kai su Arewacin ƙasar nan da garuruwan Yarabawa da na Ibo. Don haka hanya ce da ta shafi kowane ɗan ƙasar nan, wacce bai kamata mahukunta su bar ta a halin da take ciki a yanzu ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa al’umma na yin asarar biliyoyin Naira a kowane wata sakamakon lalacewar hanyar, haka ita ma gwamnati na yin asarar maƙudan kuɗaɗe a kowace rana. Don haka ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Legas da su yi haɗin gwiwa su yi gyara a hanyar. “Leburori da masu aikin sufuri da dirobobi a kullum suna cikin matsala tun lokacin da wannan hanya ta lalace. Yanzu halin da ake ciki mutane da dama na zaune babu aikin yi saboda lalacewar hanyar, don haka zaman lafiyar al’ummar wannan yanki shi ne gyaran hanyar,” inji shi.

Aminiya ta zanta da wani direban babbar mota da ke aikin ɗaukar kaya a kan hanyar ta Apapa, wanda ya so a sakaya sunansa, inda ya shaida cewa a sakamakon lalacewar hanyar direbobin manyyan motocin kan shafe mako biyu a cikin cunkoson motoci. Ya ce hakan ba ƙaramar matsala yake haifar masu ba, domin sau tari cikin dare ’yan fashi kan far masu, su ƙwace masu ’yan kuɗaɗensu da wayoyin salula.

Binciken Aminiya ya nuna cewa kanfanin da aka bai wa kwangilar gyaran hanyar a halin yanzu akwai alamun an soma gyaran hanyar a wasu ɓangare, inda aka lilliƙa alamun kamfanin da ke yin aikin, sai dai al’ummar yankin na ci gaba da kokawa bisa jinkirin aikin, abin da ke ƙara yawan cinkoson ababan hawa a hanyar.