A makon jiya, mun tattauna batun da ke tattare da almajirci, musamman mun bayyana cewa lallai hakki ne da ya rataya ga iyaye da su tarbiyantar da ’ya’yansu, su ciyar da su, su tufatar da su sannan kuma su ba su kariya; kamar kuma yadda wajibi ne su koya masu sana’a. Wannan batu gaskiya ne, haka abin yake a dukkan addinai, hatta ma dabbobi sukan aiwatar da haka. Aiki ne da Allah Ya dora wa iyaye kuma zai yi sakayya ga wanda duk ya sauke wannan nauyi, sannan zai yi azaba ga wanda ya banzatar da wannan hakki. Wannan aiki ya fi haddace Alkur’ani kima, domin haddar Alkur’ani Mustahabbi ne, wanda idan mutum bai yi ba, babu wata azaba da za a yi masa. A yayin da kuwa kula da hakkokin ’ya’ya, wajibi ne, abin da ya zama dole.
An dade ana kawo batun da ke kariya ga tsarin almajirci, inda ake tura yara wasu garuruwa ko kauyuka masu nisa daga garuruwan iyayensu. An dade ana bayyana cewa wai idan yaro ya yi nisa da gaban iyayensa, ya fi saurin daukar karatu da maida hankali. Amma inda gizo ke sakar shi ne, yadda su kansu malaman da ake ba rikon yaran, ba su mallaki dukiya ko abincin da za su ba. Wanan ya sanya za ka ga rayuwar yaran ta kasance cikin kunci da yunwa da wulakanci.
Lokaci ya yi da za mu daina yaudarar kanmu. Magance matsalolin da ke tattare da almajirci, sai mun jajirce, mun kalli al’amarin daga tushe, yadda za a yi abin da ya dace kuma mai dorewa. Gina makarantu na musamman domin almajiran tsangaya ba shi ne maganin ba kuma ba zai kawar da matsalar ba.
Babbar hanyar da ya kamata a bi wajen magance matsalar ita ce, mu sake jajircewa wajen fuskantar ilimantar da yaranmu ta hanyar karatu mai inganci. Haka kuma, lallai ne hukumomi su dauki matakan da za su samar wa iyayen yara hanyoyin dogaro da kai masu inganci, ta yadda sana’o’insu da ayyukansu za su zama ingantattu. Matakai biyu ya kamata mu fuskanta. Na farko, mu gane kuma mu tabbatar da cewa hakkin iyaye ne da na al’umma, su ilimantar da yaransu. Ita gwamnati, hakkinta ne ta samar da kayayyakin koyarwa, kamar gine-ginen makaranta, kayan aiki da malamai da sauransu. Na biyu, dole ne mu nuna da gaske muke, muna son kawar da matsalolin da ke fuskantar tsarin almajirci.
Mafi yawan lokaci, mukan magance alamun cuta ne, alhali muna barin ainahin cutar tana cin jikinmu. Idan iyayen yara suka ga cewa an banzatar da makarantun firamare na zamani, gwamnati tana mayar da hankali wajen ginawa da inganta makarantun tsangaya, da sannu za a raja’a zuwa tsangayun, wanda nan gaba kadan abin zai gundura, a yi masa yawa, sannan kuma a koma ’yar gidan jiya.
Hanyar da za a gyara matsalar almajirci ita ce, a tabbatar da cewa an taka burki ga kwararowar sabbin almajirai zuwa birane da kauyukan da ba nasu ba. daliban da suka rika suke cikin makarantun tsangaya a yanzu, a tabbatar an dora malamansu bisa tafarki mai kyau da sharudda da ka’idojin da za su bi nakwarai. Haka kuma a dauki matakan dakile tsarin baya, duk yaron da ke almajirci, a tabbatar an tanadar masa da kayayyakin bukata na rayuwa, kamar abinci, tufa, wurin kwanciya, kayan kiwon lafiya da sauransu. Haka kuma, gwamnati sai ta tallafa ta hanyoyin da suka kamata, domin tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata.
Wani mataki kuma da ya kamata a dauka shi ne, ya kamata a samar da doka, wadda za ta tabbatar da cewa kowane yaro ya tsaya garinsu ko kauyensu domin neman ilimi. Hakan mai sauki ne, musamman ganin cewa a yanzu ilimi ya bunkasa, babu wani gari ko kauyen da za ka samu, inda babu malaman addini da za su iya ilimantar da yara. Ta haka, yaran za su kasance kusa da iyayensu, inda za su samu kulawa ta fuskar abinci, kiwon lafiya, sutura da kuma koya tarbiyya.
A nan, ba ana nufin a hana masu sha’awar fadada karatu zuwa wasu garuruwa ba ne. Idan dalibi ya mallaki hankalinsa kuma yana sha’awar fadada karatunsa, yana iya tafiya duk inda yake so, domin kuwa ya girma, don haka zai iya daukar dawainiyar kansa.
A yanzu ya kamata mu zo kuma mu fuskanci wannan batun, wanda kowa ke tsoron furtawa. Shin ilimin Alkur’ani ne kadai ya wajaba a kanmu kuma shi ne kadai ya kamata mu koya kuma ta hanyar almajirci? Ko kuwa muna ganin ya kamata a saka karatun Alkur’ani a manhajar makarantunmu na zamani? Ni dai ban ce malamin addini ne ni ba, (idan na yi kuskure, Allah yafe mani), amma ina ganin da wannan ilimin ne kadai aka wajabta mana mu nema, da Allah Ya fada mana. Sai dai ni kam abin da na fahimta shi ne, wajibi ne gare mu mu nemi ilimi kowane iri, domin kuwa ayar farko ma da aka saukar wa Manzo (SAW) ita ce mai cewa ‘Yi Karatu.’ Kuma an umurce mu da cewa mu nemi ilimi koda zuwa birnin Sin ne, inda ake ganin kasa ce mai nisan gaske.
Shi ilimi, nemansa ma aikin ibada ne, don haka bai kamata mu tsaya ga ilimi iri daya ba kawai. Kamata ya yi mu saka dukkan al’amuran ilimin addinanmu cikin manhajar makarantunmu. Mu inganta yaranmu da duk ilimin da zai taimaki rayuwarsu ta duniya da lahira. Wannan shi ne!