Har yanzu ana ci gaba da tafka muhawara game da tsarin almajiranci a kasar nan, inda wadansu suke ganin akwai bukatar a sake wa tsarin fasali wadansu kuma suna ganin a bar shi yadda yake.
Almajiranci ya samo asali ne daga kalmar “almuhajir” na Larabci, wanda ke nufin ‘wanda ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon Musulunci. Daga nan sai daliban da ke barin garuruwansu domin neman ilimin addinin Musulunci su ma aka rika kiransu ‘almuhajir’ din, wanda a kasar Hausa aka rika kiran wanda ya yi haka da almajiri.
A karkashin wannan tsari dalibai suna barin garurruwansu ne su tafi wani gari domin neman ilimi a wurin wani malami, wani malamin kuma yakan kwashi daliban nasa ne ya tafi yawo da su gari-gari domin ci-rani.
A irin wannan halin mutanen gari sukan taimaka wa malamin tare da dalibansa ta hanyar ba su masauki da kuma abinci har ma da sutura, saboda su baki ne wadanda suka yi hijira daga garurruwansu domin neman ilimi. A dalilin haka ne sunan almajirai ya kama irin wadannan daliban. Haka nan tsarin yake ta tafiya tare da fadada har aka kawo wannan lokaci.
Da farko wadanda suke fita neman irin wannan ilimi matasa ne zuwa sama, wadanda suke da karfin neman abin da za su ci, amma zuwa yanzu sai lamarin ya canja inda ake samun kananan yara sosai a cikin tsarin.
Yanzu ana cikin wani lokaci mai wahala da aka mayar da rayukan mutane banza, inda mutane suke tafiya a cikin tsoro saboda sace mutane da ake yi ana tsafi da su, kuma babu wanda ya tsira daga hakan, babba da yaro, mace da namiji.
A irin wannan hali ne za ka ga yara kanana iyayensu sun tura su almajiranci inda suke yawo kwararo-kwararo suna neman abin da za su ci, wanda a sakamakon hakan suke fuskantar matsaloli da wulakanci iri-iri. Wani lokacin su fada hannun matsafa su hallaka su, wani lokaci su fada hannun wadanda za su lalata su ta hanyar yi masu fyade ko kuma a wulakanta su kafin a ba su abinci, kuma abincin da bai kamata a ba mutum ba. Haka za ka ga yara suna watangaririya a titi suna neman abin da za su ci.
Wata rana na ga wani yaro da bai wuce shekara shida ba yana bara, da kyar yake magana saboda yunwa ta gallabe shi, ya kasa yin barar a tsaye, sai zaunawa ya yi yana cewa “Iya yunwa nake ji! Iya yunwa ba ta da hankali!” Abin gwanin ban tausayi.
Wadansu malamai suke hure wa iyayen yara kunne cewa yaro ba zai samu karatu ba sai ya sha wahala, ya ci abincin da ake kira ‘dan dago-dago,’ ya sha tokar makaranta, wato ya yi bidi-bidi cikin toka, sannan wai karatu zai zauna.
Wannan dabara ce kawai da irin wadannan malaman suka fito da ita domin su rika amfani da ’ya’yan mutane suna bautar da su domin su samu abinci, shi ya sanya yaro sai ya kwashe shekaru yana wahala, duk ya tsumbure kuma babu wani karatun kirki da ya samu. Domin kuwa yaron da ya zauna a gaban iyayensa ya yi karatu ilimin da zai samu ya fi na yaron da ya fita karatu ta hanyar almajiranci.
Idan a baya ana tafiya nesa domin neman ilimi saboda karancin malamai, yanzu nesa ta zo kusa, akwai malamai masana a dukkan manyan garurruwan da ke kusa da kowane kauye, ba sai an tafi nesa ba za a iya samun karatu yanzu, kuma cikin sauki ba sai an wahala sosai ba, domin an saukaka hanyoyin karatun saboda ci gaban zamani.
Saboda haka ba daidai ba ne a dage cewa ba za a canja tsarin karatun da aka gada daga iyaye da kakanni ba, wannan kuskure ne babba, komai yana tafiya ne daidai da zamani.
Yaron da ya zauna a gida ya yi karatu ya fi saurin haddace Alkur’ani fiye da wanda ya bar gida ya tafi almajiranci, domin wanda ya yi karatu a gaban iyayensa ya fi samun kwanciyar hankali fiye da wanda ya rabu da su, kuma karatu ba ya samuwa sai da kwanciyar hankali tare da natsuwa.
Abin takaici kuma shi ne mafi yawan malaman da suke goyon bayan a ci gaba da amfani da tsarin almajirancin nan ’ya’yansu ba su yin bara, suna tare da ’ya’yansu suna karantar da su, sauran ’ya’yan mutane kuma suna yi musu bauta.
Su kuma iyayen da suke tura ’ya’yansu almajirancin ga dukkan alamu suna yin haka ne domin su kauce daga nauyin da aka dora musu na tarbiyyarsu, sun dauka haihuwar yaran ne kawai hakkinsu, babu ruwansu da tarbiyyarsu da sauran hakkokinsu. Sai tura wa malami yara ba tare kai musu ziyara ba.
Akwai wani yaro karami da na gani yana bara a gidan mai, ya zo ya gaishe ni, sai ya ce mini ‘ ba ka gane ni ba ko? ‘Na ce masa ‘kwarai,’ sai ya ce ‘ ni dan gidan Alhaji wane ne.’ Ashe unguwarmu daya da shi. Da na tambaye shi me ya sa yake bara, sai ya ce an tura shi karatun allo ne a nan garin Kaduna da mahaifan nasa suke kuma an ce kada ya rika zuwa gida. Gidan da wannan yaron ya fito suna da rufin asiri daidai gwargwado, har motocin haya suke da su, amma sun tura yaro karami almajiranci yana bara a garin da suke kuma suka hana shi zuwa gida, saboda sun yi imanin ta haka ne kawai yaron zai samu karatu. Amma sai ga shi yana gararamba a titi yana neman abin da zai ci, alhali gidansu suna da abincin da za su ba shi ba sai ya yi bara ya wulakanta kafin ya samu ba.
Bara lalura ce, sai dole ake yi, kuma ana ba Sarki kyauta, amma ba a ba shi sadaka, saboda kaskanci ne, idan mutum ya yi gardama ya dauki wani abu ya kai fada ya ce ya kawo wa Sarki sadaka ce ya ga yadda fadawa za su yi biji-biji da shi.
Saboda haka tunda kida ya canja ya kamata rawa ma ta canja, a yi hakuri a bari a zamanantar da tsarin almajiranci domin a samu biyan bukata. Hausawa na cewa “Kowa ya ki zamani ya ki Allah!”