Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) da hadin guiwar Shugaban Karamar Hukumar Fataskum da wakilcin Masarautar Fika sun kaddamar da shirin na bai wa almajirai kayan Sallah a garin Fataskum.
An kaddamar da shirin ne a tsangayar Malam Bello dake unguwar Jaji dake garin na Fataskum.
Kimanin tsangayu 271 daga Kananan Hukumomi bakwai na Jihar da kuma almajirai 12,000 ne ake sa ran za su amfana da tallafin a karon farko.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, Shugaban Karamar Hukumar Fataskum, Salisu Muktari cewa ya yi tallafin ya zo a lokacin da ya dace.
Shugaban ya ce yunkurin na cikin irin hobbasan da gwamnatin Gwamna ai Mala Buni ke yi wajen saukakewa almajirai kuncin rayuwa da wasu makarantun tsangaya a Jihar a yau.
Alhaji Salisu ya kuma kira ga shugabannin tsangayun da su kamanta adalci wajen raba kayan abincin da tufafin ga yaran da aka ware domin su kamar yadda Gwamna ya ba da unurni.
A nasa jawabin, Shugaban hukumar ta SEMA Dokta Muhammad Goje, ya ce shirin daya ne daga irin tsarin da Gwamnan na shiga tsakani don ganin an kawo sauyi a tsarin almajiranci a Jihar.
Dokta Goje, ya kuma ce kowacce tsangaya cikin 271 da aka zabo za ta samu isasshen abincin da akalla almajirai 50 zuwa 100 za su ci a ranar Sallah da kuma karin kayan Sallah na yawan wadanan almajiran.
Ya ce babbar hikimar ita ce ta ganin basu fita bara ba a ranar Sallah
Sauran abubuwan da aka gudanar a wajen bikin sun hada da adduo’in samun da zaman lafiya a masarautar Fika da Jihar Yobe da ma kasa baki daya, da kuma karatun Alkur’ani.