✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Turakin Saminaka rasuwa

Allah Ya yi wa Turakin Saminaka kuma Mataimakin Ma’ajin Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna Alhaji Ado Abubakar Saminaka rasuwa, a daren Juma’ar da ta gabata.…

Allah Ya yi wa Turakin Saminaka kuma Mataimakin Ma’ajin Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna Alhaji Ado Abubakar Saminaka rasuwa, a daren Juma’ar da ta gabata.

Marigayin, wanda babban jigo ne a siyasar Karamar Hukumar Lere da Jihar Kaduna, ya rasu yana da shekara 59. Kuma ya rasu ya bar matan aure hudu da ’ya’ya 21 da jikoki da ’yan uwa da dama.

Rasuwar marigayin ta yi matukar girgiza garin Saminaka da Karamar Hukumar Lere baki daya.

Wadansu mutanen da suka zanta da wakilinmu a wajen jana’izar marigayin, da aka gudanar a garin Saminaka a safiyar Juma’ar da ta gabata, sun bayyana cewa ba su taba ganin yawan mutane a wajen jana’iza a garin kamar ta marigayin ba.

Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin ’yan uwan marigayin, Tafidan Saminaka Alhaji Musa Abubakar ya bayyana cewa rasuwar marigayin wani babban rashi ne ga al’ummar Karamar Hukumar Lere da Jihar Kaduna baki daya.

Ya ce marigayin wani babban bangon jigina ne ga al’umma baki daya, ba wai ga ’yan uwansa kadai ba. “Domin yana taimaka wa dukan mutanen da suka zo neman taimako wajensa, ba tare da nuna banbanci ba,” inji shi.

Daga cikin manyan mutanen da suka kawo ziyarar ta’aziya ga iyalan marigayin, akwai Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna kuma dan takarar kujerar Majalisar Dattawa, Shiyya ta Daya, a karkashin Jam’iyyar APC Alhaji Sulaiman Kwari da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Bashir  Sa’idu da Babban Jojin Jihar Kaduna Alhaji Mannir Ladan da manyan ’yan siyasar Karamar Hukumar Lere da   shugabannin kananan hukumomi da dama na Jihar Kaduna da manyan jami’an gwamnati da ’yan kwangila da sauransu.