✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Sharu Rabi’u Usman Baba rasuwa

Da sanyin safiyar jiya Alhamis, ce muka samu rahoton Allah Ya yi wa fitaccen sha’irin nan, Sharu Rabi’u Usman Baba rasuwa. Bayanai sun nuna an…

Da sanyin safiyar jiya Alhamis, ce muka samu rahoton Allah Ya yi wa fitaccen sha’irin nan, Sharu Rabi’u Usman Baba rasuwa.

Bayanai sun nuna an gudanar da jan’izarsa a gidansa da ke Kofa ta Biyu (Second Gate) da ke Unguwar Janbulo a cikin Birnin Kano.

Kafin rasuwarsa, Rabi’u Usman Baba ya shahara wajen rera wakokin yabon Annabi (SAW) da iyalansa, inda har ya ciri tuta kuma ya zamo Shugaban Kungiyar Mawakan Manzon Allah (SAW), wato Shu’ara’ul Islam ta Najeriya baki daya.

Zuwa yanzu dai jama’a da dama na ci gaba da bayyana alhininsu game da rasuwar babban sha’irin, tare da jimamin rashinsa, musamman lura da yadda wakokinsa suka yi tasiri a tsakanin mabiya Darikar Tijjaniyya da Kadiriyya.

Wadansu daga cikin fitattun wakokin Rabi’u Usman Baba sun hada da Babu tantama da Tsumagiya da Sha Yabo da Majalisi da Sada Zumunci da Tambaya da Sharifai da Fadima da Garkuwa da Batijaniyya da Bakadiriya da Fiyayya da Sayyadil Wara da Zuma. da sauransu