✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa limamin Jere rasuwa

Cikin ’ya’yansa har da zababben Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman.

Allah Ya yi wa limamin Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, Malam Adamu Usman, rasuwa a wannan Lahadin.

Adamu, ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda daya daga cikin iyalansa, Abbas Bello Ja’afar ya shaida wa Aminiya.

Ya ce mahaifin nasu ya rasu bayan jinyar sati daya, kuma an yi jana’izarsa bayan sallar Azahar kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama ciki har da zababben Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman da kuma Durbin Jere, Alhaji Aminu Adamu, ma’aikaci a Muryar Najeriya (VON).

Malam Adamu ya rasu yana da shekara 77 a duniya.

%d bloggers like this: