✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa babbar jikar Sardauna rasuwa

Marigayiyar 'ya ce ga marigayi Wamban Kano, Abubakar Dan Maje.

Allah ya yi wa babbar jikar Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Hajiya Hadiza, rasuwa.

Hajiya Hadiza ta rasu a Sakkwato bayan fama da wata gajeriyar rashin lafiya.

Marigayiyar, ’ya ce ga marigayi Wamban Kano Abubakar Dan Maje, babban da ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I.

An haifi Hajiya Hadiza a shekarar 1960, kuma ta auri tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Shehu Kangiwa

Ta rasu ta bar ’ya’ya uku, sannan an yi jana’izarta tare da birneta a gidan Sardauna da ke kan titin Diori Hammani, a Jihar Sakkwato.