Alhaji Idris Bayero, wanda aka fi sani da Barden Kano kuma hakimin Bichi, ya rasu yana da shekara 90.
Shi ne babban ɗan marigayi Sarkin Kano, Abdullahi Bayero, wanda ya yi mulki daga 1926 zuwa 1953.
- Farashin kayan abinci da sufuri ya karu a Taraba
- Harajin da ake karɓa a Najeriya ya yi kaɗan — Bill Gates
Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II ne, ya jagoranci sallar jana’izar marigayin a fadar Kofar Kudu, tare da ɗimbin jama’a.
An fara 1990 naɗa Alhaji Idris Bayero a matsayin Ɗan Darman Kano kuma hakimin Rimin Gado ta hannun ɗan uwansa, marigayi Sarki Ado Bayero, wanda ya yi mulki daga 1963 zuwa 2014.
Bayan shekara biyu, a 1992, an ƙara masa matsayi zuwa Ɗan Buram kuma daga baya aka naɗa shi a matsayin Barde sannan daga baya aka naɗa shi hakimin Bichi.
An haifi Alhaji Idris Bayero a shekarar 1934, ya halarci Makarantar Firamare ta Kofar Kudu, ya yi makarantar Kano Middle School da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ya yi aiki na ɗan lokaci a Hukumar Gargajiya ta Kano, daga baya ya zama Sakatare na Majalisar Masarautar Kano.
Ya yi aiki a Bankin Arab na Najeriya na ɗan lokaci kafin yi masa muƙamin hakimi.
A shekarar 2019, ya yi murabus daga matsayinsa na hakimi bayan ɗaga darajar Bichi zuwa masarauta da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
A wancan lokacin gwamnam ya naɗa Aminu Ado Bayero, a matsayin Sarkin Bichi.
Sai dai, an sake dawo da Alhaji Idris Bayero a matsayin hakimin Bichi a watan Yunin 2024, bayan Sarki Sanusi, bayan rushe masarautun Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Alhaji Idris Bayero ya bar mata da yara 11, da kuma jikoki da yawa.