✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Dan Isan Zazzau rasuwa

Yariman ya rasu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Allah Ya yi wa Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idirs, rasuwa a gidansa da ke Zariya a Jihar Kaduna da yammacin ranar Talata.

Dan Isan Zazzau, ya rasu ne lokacin da yake barci.

Jami’in hulɗa da jama’a na masarautar Mallam Abdullahi Aliyu Kwarbai ne, ya tabbatar da rasuwar.

Kafin rasuwarsa, Umar Shehu Idris ya kasance Mataimakin Sakatare a Majalisar Masarautar Zazzau.

Ya rasu yana da shekara 41, ya bar mata biyu da yara biyu.

Mahaifiyarsa ta kasance mata ga tsohon Sarkin Zazzau, Dokta Shehu Idris, kuma mahaifiyar matar Sarkin Zazzau na yanzu, Ahmed Nuhu Bamalli, wadda ta rasu kwana 39 da suka gabata.