A safiyar Litinin ce Allah ya yi wa Ajiyan Gombe kuma Hakimin Kwami da ke Jihar ta Gombe, Alhaji Haruna Abdullahi rasuwa, yana da shekara 94 a duniya.
Marigayin, wanda yaya ne ga tsohon Ministan Ilimi, kuma Jakadan Najeriya a Malesiya, Ambasada Ibrahim Yerima Abdullahi ya rasu ne bayan ya sha fama da doguwar jinya.
- Harin Gidan Yarin Kuje: An kama fursuna daya a wata tashar mota a Abuja
- Dalilin da na yi aikin Hajji a Kano —Maniyyaci
ya rasu a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe.
Kafin rasuwarsa, Hakimin ya shafe shekara 53 a kan gadon sarauta, kuma an yi masa shaida a matsayin mutum ne mai ilimi da sanin ya kamata da yake kokarin hada kan jama’ar sa a kowanne lokaci.
An shirya gudanar da sallar jana’izar marigayin ne a masarautar Kwami da ke garin Malam Sidi da misalin karfe 2:30 na ranar nan.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yiwa masarautar Gombe da ta Kwami da ma daukacin al’ummar jihar ta’aziyar rasuwar ta Ajiyan Gombe.
Ta’aziyar da ke dauke a wata takardar mai dauke da sanya hannun Babban Daraktan Yada labarai na Gwamnan, Isma’il Uba Misilli, ta nuna kaduwar Gwamnan kan babban rashiN, inda ya ce mutuwarsa za ta bar babban gibi mai wuyar cikewa.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya hori iyalan Marigayin da cewa su yi koyi da irin kyawawan halayensa domin mutum ne haziki.