✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya ja zamanin Sarkin Ban Kano Alhaji Muktar Adnan

A cikin makon da ya gabata aka gudanar da addu`o`i da hirarraki na musamman da manema labarai a garin danbatta, hekwatar karamar Hukumar danbatta da…

A cikin makon da ya gabata aka gudanar da addu`o`i da hirarraki na musamman da manema labarai a garin danbatta, hekwatar karamar Hukumar danbatta da ke cikin Jihar Kano a zaman cika shekaru 60 cif-cif a kan karagar mulki da Alhaji Mukhtar Adnan, Hakimin danbatta kuma Sarkin Ban Kano ya yi.
Alhaji Muktar ya zama Hakimim danbatta kuma Sarkin Ban Kano a shekarar 1954, wadda kuma ta yi daidai da shekarar da aka zabe shi a zaman dan Majalisar Wakilai ta Tarayya ta farko da ke Ikko, yana wakiltarta gundumomin kiru da karaye a lokacin da Turawa ke mulkin kasar nan, har kuma zuwa jamhuriya ta farko, wadda aka yi tsakanin shekarun 1960 zuwa 1966.
dan takaitaccen tarihin wannan dan taliki Basarake kuma dan siyasa, ya nuna yana daga cikin Hakimai hudu (Madaki da Sarkin Bai da Makama da Sarkin Dawaki mai Tuta) masu zaben Sarkin Kano, wanda kuma a yau shi kadai yake raye daga cikin wadanda suka zabi Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayaro, a matsayin Sarki a shekarar 1963. Kazalika yana daga cikin `yan siyasar farko na kasar nan da suka shige gaba wajen samo wa kasar `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. A bana yana da shekaru 88, a duniya. Shi ne Hakimin da ya fi kowane Hakimi a nan Arewa tsawon kwana kan karagar mulki, inda ya shekara 60, wadda a Kudanci da Gabashin kasar nan ma, ina jin sai an tona.
An haifi Alhaji Muktar Adnan a unguwar kofar Gabas ta garin danbatta a shekarar 1926, kuma kamar yadda yake a al`adar Hausawa musulmi, tun yana dan shekaru 4 da haihuwa ya shiga makarantar allo, don samun karatun Alkur`ani mai tsaki. A lokacin da ya kai shekara 9, aka sa shi makarantar Elmentare ta danbatta, tsakanin shekarun 1935 zuwa 1939. A tsakanin shekarun 1939 zuwa 1944, ya zarce zuwa makarantar Midil ta Kano ta wancan lokacin da a yau ake kira Kwalejin Rumfa, makarantar da ta zama daya tilo a lokaci mai tsawo, inda duk wani dan asalin tsohon lardin Kano, (lardi da a yau ya kunshi jihohin Kano da Jigawa), a nan ya yi karatunsa na boko.
Bayan kammala makarantar Midil ta Kano, bisa umurnin mahaifinsa, wanda yake Hakimin Danbatta kuma Sarkin Ban Kano, ya koma garin danbatta, inda ya fara aiki a zaman magatakarda ga mahaifinsa. Bayan ya yi shekara daya, a zaman Malamin Hakimi, sai aka tura shi Kwalejin Horar da Akawuna da ke Zariya, inda ya nuna matukar kwazo, don haka maimakon ya koma bakin aikinsa na danbatta, ko En`en Kano ta waccan lokacin, sai aka wuce da shi Kaduna a cikin aikin gwamnatin Arewa, inda aka ba shi mukamin mai binciken kudi (odita). A kan wannan mukami ne ya yi aiki a garuruwan Zariya da Kano. Daga bisani kuma sai ya dawo da aiki a En`en Kano, a matsayin mataimakin Akanta.
Shigowar harkokin siyasa da Turawan mulkin mallaka suka bullo da ita a zaman shirye-shiryen ba da mulkin kai, a shekarar 1954, an zabi Alhaji Muktar Adnan a matsayin dan Majalisar Wakilai  ta Tarayya mai wakiltar mazabar kiru da karaye, Majalisar da ya zauna har karo biyu, ko in ce har zuwa lokacin da sojoji suka yi juyin mulkin farko na ranar 15 ga watan Janairun 1966, wanda yin wancan juyin mulki ya kawo karshen harkokin siyasar jamhuriyar farko, hakan kuma ya sanya mai girma Sarkin Ban Kano ya dawo kan kujerarsa ta Hakimin danbatta, sarautar da da ma yake rike da ita a dai shekarar da ya tafi Majalisar Wakilan.
A tsawon shekaru 12 da mai girma Sarkin Ban Kano ya yi a Majalisar Wakilai ta Tarayya, shi ne Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar, mukamin da ya dana a cikin yana da karancin shekaru, sannan da ilmin boko, abubuwan da suka ba shi damar kasancewarsa tamfar wata a daren 15, a Majalisar, ta yadda idan za a yi wani kuduri mai nauyi, irin su Sarkin Bai akan sa gaba su gabatar. Alal misali, a shekarar 1962, da madugun adawa na wancan lokacin Cif Obafemi Awolowo, ya je London ya bayar da wata lacca, wadda a cikinta ya soki gwamnatin tarayya a kan tana da rauni don haka ba ta dace da a ce ita ke gudanar da mulki ba, Alhaji Muktar Adnan aka sanya ya gabatar da wani kuduri da ya zama martani da kuma yin tir da Allah-wadai da abin da Cif Awolowo ya yi a kasar ta Birtaniya, wadda suka kalla zubar da mutuncin kasa a idanun duniya. Duk da yake `yan adawa sun yi kokarin su hana samun nasarar wancan kuduri, daga karshe sai da kudurin ya kai labari, Majalisa dai ta yi tir da Allah-wadai da abin da Madugun adawa Cif Awolowo ya yi a London.
Tirkashi! Mai karatu, ka ji siyasa ta kishin kasa, wadda yanzu da masu mulkin da `yan adawar sun fi sukar junansu a kasashen waje.
Idan muka komo kan ayyukan ganin kyautatuwar rayuwar talakawansa da Alhaji Muktar Adnan ya yi a cikin mulkinsa na shekaru 60, wadanada yake alfahari da su, akwai batun ganin habakar ilmin addini da na zamani a Jihar Kano da masarautarsa ta danbatta. Kasancewarsa Kwamishinan Ilmin jihar na farko, da kuma ya samu tsawon shekaru 8, a zamanin gwamnatin marigayi Alhaji Audu Bako, a tashin farko suka kafa makarantun gaba da firamare 24, a lokacin da suka taras da sabuwar jihar tana da irin wadancan makarantu guuda 7 kacal.
A yau, ba sai gobe ba, Sarkin Ban na Kano yana alfahari da kasancewar a  duk kananan Hukumomin Jihar Kano 44, mutanen kananan hukumomin cikin birni da kewaye kadai suka fi mutanen karanmar hukumarsa yawan masu ilimi, haka kuma ya faru ne bisa ga irin yadda ya dage a kan lallai sai talakawansa sun yi ilimi. Haka batun yake a kan harkokin noma da kiwo.
A takaicen-takaitawa mai karatu, ka iya cewa rayuwa irin ta su Alhaji Muktar Adnan ta yi kyau, idan ka yi la`akari da yadda ya taso cikin gwagwarmayar ganin ingantuwar rayuwar al`aumma, musamman a kan ilimi da noma. Ayyuka biyun da mutane, har gobe suka ce Sarkin Ban na Kano ba ya sanya da su.
Allah Ya kara wa Sarkin Bai lafiya da jinkiri mai amfani, Ya kuma duba bayansa, amin summa amin.