✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah mai hana kunya ranar gaskiya (2)

Masu iya magana sun ce dadi na da gobe saurin zuwa to wannan fa goben jiya ce, kafin goben kiyama. Idan barayi sun fi shugaban…

Masu iya magana sun ce dadi na da gobe saurin zuwa to wannan fa goben jiya ce, kafin goben kiyama. Idan barayi sun fi shugaban kasa yawa, mu da suka yi wa satar mun fi su yawa ninkin ba ninkin. Kada ma su yi tunanin idan Buhari ya gama suna da wata dama, duk wanda zai biyo bayan Buhari sai dai ya fi Buhari – Insha Allah. Kayan Allah ba ya karewa, komai lalacewar duniya ba a rasa na Allah. Duk lalacewar da Ghana ta yi a baya sai da J.J Rawlings ya zo ya yi mata saiti. Allah ya ba mu ikon gyarawa, amin.
Allah Sarkin na baka rata, kamar yadda duk iya alkalancin Alkali, idan wani ya kashe masa mahaifi a gabansa, ba zai hukunta shi ba, har sai wani daban ya kawo kara, wasu sun ba da shaida kamar yadda doka ta tanada sannan ya yi hukuncin da ya dace. Haka ko ni kadai maganganun da na yi akan azzalumai, barayin shugabannin Najeriya a Gidajen Radio na Duniya, musamman BBC da bOA da bOG da RFI da sauransu na tsawon shekaru fiye da talatin (30) zuwa yau sun isa kawo kara gurin Gwamnati maici, haka kuma shugabannin EFCC musamman Mal. Nuhu Ribadu da Farida Waziri da maici yanzu da wasikar Obasanjo mai shafi 18 zuwa ga Jonathan da maganar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Malam Sanusi Lamido Sanusi sun isa shaidu akan duk irin maganganun da na yi fiye da shekaru talatin (30) baya zuwa yanzu saboda haka nake kira ga gwamnati ta nemi duk maganganun da na yi akan shugabanni da irin satar da suka yi mana suka rusa mana masana’antu da kasuwanci da hakar ma’adanai da ayyukan noma da kiwo da sauran sana’o’inmu na hannu da bankuna da wasunmu da suka kashe mana, a biya mu diyya da abin da aka kwato daga wajeninsu kafin a kashe su. Ba kamar yadda wasu na gindin gwamnati suke ganinmu ba mu da wani hakki a kasar nan ba sai su. Babu ruwansu da matsalolin da muke ciki. Daga jami’an gwamnati sai ‘yan siyasa. Allah cewa, ya yi ya ajiye arziki a saye da sayarwa, kamar yadda na gada, tun daga noma da kiwo, cinikin gyada da harkar fatu da jima, na yi aiki a kamfanin Faransa CFAO, na yi shugabancin kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu da ma’adanai da ayyukan gona. Babu kasar da ban je ba a Turai da Amurka da Gabas ta Tsakiya da Gabas mai Nisa (Far East), amma saboda rigimar da nake yi da barayin shugabanni babu irin batani da ba su yi ba; a ce ni bakin ciki nike yi Allah ya yi wa barayin gwamnati arziki, wasu su ce ina bata wa barayin suna ne don bana cikin su-a gwamnati, wasu ma suna cewa ni dan gurguzu ne ba na son kowa ya yi arziki, wasu su rika yi min zunde suna cewa, wai ni matsiyaci ne, ba cin sun tsiyatamu, koda suka kasa samun hadin kaina shi ne suka fara kamani suna tsare ni, har sai da Allah ya kawar mana da su. Ina dada nanatawa, idan barayin gwamnati suna ganin sun fi shugaban kasa yawa mu da suka yi wa satar mun fi su yawa ninkin ba ninkin ka da su yi fatan akai jallin fito- na -fto tsakanin barayi da masu kaya a Najeriya, abin ba zai yi musu kyau ba, gara ma a ja layi tsakanin barayi da masu kaya kowa ya san matsayinsa a zabe  da EFCC da Tribunal da kwamitocin kwato kudi da kadarori da aka wawashe mana, mai karfin shari’a, da hukuncin da zai biyo baya akan kowane barawon gwamnati komai matsayinsa.
Wasun mu da yawa mun ja baya ne, ganin yadda barayin farko na tun fiye da shekara talatin (30),  musamman sojojin cikinsu su ne suke jan akalar harkokin siyasa, suna yin amfani da kudin da suka sata suna nada wadanda suke so don su wakilce su. Bacin kamfanonin da suka kafa suka dora yaransu suna gudanar musu da su, haka bankuna da masana’antu – gida da waje. Kamar yadda kowa ya gani Ibrahim Babangida da Abdussalami Abubakar da Olusegun Obasanjo su ne masu PDP, duk wanda ya zama gwamna ko sanata ko wakili a tarayya yaransu ne, har da na wasu jam’iyyun balle PDP, shi ya sa suka yi ta yin abin da suka ga dama. Allah ne kawai ya shigo mana al’amarin, mulkin ya kubuce musu. Babban farin cikina da Allah ya sa wani sojan da ba sa so ne (Muhammadu Buhari) da ya san sirrinsu fiye da kowa, ya zama shugaban kasa na farar hula, mai cikakken iko, yake da damar ya gane duk munafukan da suka kewaye shi ada, ta yadda zai gane irin yadda zai yi mu’amila da sababbin abokan aikinsa. Har ya kai ga burinsa na kwatowa kowa hakkinsa da irin hukuncin da za a yi wa kowanne barawo komai girmansa.
Babban hadarin da ake ciki a Najeriya da duniya baki daya bai wuce da aka bari wasu suke fakewa da addini suna halatta haram da sunan ilimin badini ba, su a gurinsu komai halal ne – idan suka kashe mutum halal ne, idan suka yi sata halal ne, idan suka yi zina da luwadi da madigo duk halal ne a gurinsu. Babu ruwansu da kowacce dokar Allah, duk abinda Allah ya haramta su halal ne a gurinsu. Har akwai malamai masu ba da lakani, wai idan mutum ya yi luwadi zai zama mai mulki, idan dan sarauta ne zai gaji sarauta, idan dan kasuwa ne zai yi arziki mai yawa. Ta haka ne mulki da sarauta da kasuwanci suka gurbata, aka gurbata rayuwar matasa – samari da ‘yan mata, har da matan aure. Shi yasa kotuna da alkalai da jami’an tsaro ba sa iya yin aikinsu yadda ya kamata bisa doron shari’a, saboda yawancin masu mulkin da sarakuna da ‘yan kasuwa, musamman irin malaman da suka dora su a kan wannan akida ta ilimin badini – komai halal ne, babu wani haram, sune mafiya yawa.
Masu iya Magana dai sun ce, duk abin da ya gagara hanuwa, masu ikon hanawar ne suke yi. Saboda haka duk masu rike da madafun iko a yanzu; shugabanni da  sarakuna da attajirai da malamai, idan sun bambanta da wadancan sai su dauki matakai na inganta shari’a da zartar da hukunci akan duk wanda ya kashe wani da wanda ya yi sata da wanda ya yi zina da luwadi da madigo da sauransu, kamar yadda Allah ya yi umarni a cikin littafinsa mai tsarki. Maimakon dokokin da wasu masu sabo suka kirkiro, dokoki da suka yi karo da na Allah, ana barin na Allah ana aiki da nasu. Bacin Allah ne ya halicce mu ba wasu ba.
Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN)
08060116666, 08023106666