✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah kawo ruwa

Wani Inyamuri ne aka wayi gari da ruwan sama har yamma ba a dauke ba, bai samu damar bude shagonsa ba. Da dare, bayan ruwa…

Wani Inyamuri ne aka wayi gari da ruwan sama har yamma ba a dauke ba, bai samu damar bude shagonsa ba. Da dare, bayan ruwa ya dauke sai ya bude shagon yana kasa kaya, sai ga wani Bahaushe ya zo sayayya. Can sai aka buga walkiya da tsawa, Bahaushe ya ce: “Allah kawo mana ruwa!” Cikin fushi Inyamurin nan ya ce: “Wanda aka yi tun da safe, me ka yi da shi?”
Daga Sunusi NNPC, 08034367040