✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Alkawari daya ne ba mu cika wa Shekarau ba — Kwankwaso

Ya ce babu wani alkawari da ba su cika wa Shekarau ba, sai guda daya

Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau da har zai sa ya fice daga jam’iyyar.

Kwankwaso na tsokaci ne kan rahotannin rashin jituwar da take tsakanin tsoffin Gwamnonin na Kano biyu wanda har ake rade-radin Shekarau zai fice daga NNPP.

A wata hirarsa da BBC ranar Laraba, Kwankwason ya yi ya ce duk abin da ake fada ba gaskiya ba ne.

“[A lokacin da suka shigo jam’iyyar] Babu sharadin da suka gindaya mana da ba mu cika ba, illa batun ’yan takara. Mun yi iya bakin kokarinmu mu cika wannan sharadin amma lokaci ne ya kure mana,” inji Kwakwaso.

Sannan sai ya ce, mutanen da duk Shekarau ya zo da su daga APC masu son yin takara, lokaci ya kure da INEC ba za ta karbe su ba.

Sai dai ya ce sun yi wa mutanen Shekarau alkawarin manyan mukamai  gwamnati idan jama’iyyarsu ta kafa gwamnati a 2023.