✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, ya ajiye mukaminsa

Ajiye aikin na zuwa ne lokacin da ake masa zarge-zargen rashawa

Alkalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, ya ajiye mukaminsa a daidai lokacin da alkalan Kotun Koli ke ci gaba da yi masa zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Aminiya ta gano cewa alakalan kotun kolin su 14 ne suka rubuta masa wasika suna korafi a kan rike musu kudadensu na alawus-alawus ad kuma zargin hana su zuwa samun horo.

Alkalan sun yi zargin cewa Ibrahim Tanko ya toshe musu kudaden alawu-alawus  ba tare da wani dalili ba.

Su kuma i zargin cewa Alkalin Alkalan ya yi wa iyalansa da ma’akatan da ke karkashinsa tanadin tafiya kasashen waje, amma su kuma ya hana su damar.

Daga bisani dai ya mayar da martani inda ya bayar da bayanai kan zarge-zargen alkalan, inda ya ce bai shiga cece-kuce da su ba, sai lokacin da wasikar ta bulla a duniya.

Tanko dai ya zama Alkalin Alkalai a 2019, bayan cire magajinsa, Samuel Walter Onnoghen, kan zarge-zargen cin hanci.

%d bloggers like this: