Alkalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, ya ajiye mukaminsa a daidai lokacin da alkalan Kotun Koli ke ci gaba da yi masa zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Aminiya ta gano cewa alakalan kotun kolin su 14 ne suka rubuta masa wasika suna korafi a kan rike musu kudadensu na alawus-alawus ad kuma zargin hana su zuwa samun horo.
- Bankuna sun damfare mu biliyan 22 cikin wata guda – MTN
- Yadda muka ceto almajirai 21 daga coci a Jos – DSS
Alkalan sun yi zargin cewa Ibrahim Tanko ya toshe musu kudaden alawu-alawus ba tare da wani dalili ba.
Su kuma i zargin cewa Alkalin Alkalan ya yi wa iyalansa da ma’akatan da ke karkashinsa tanadin tafiya kasashen waje, amma su kuma ya hana su damar.
Daga bisani dai ya mayar da martani inda ya bayar da bayanai kan zarge-zargen alkalan, inda ya ce bai shiga cece-kuce da su ba, sai lokacin da wasikar ta bulla a duniya.
Tanko dai ya zama Alkalin Alkalai a 2019, bayan cire magajinsa, Samuel Walter Onnoghen, kan zarge-zargen cin hanci.