Alkalin wata kotun Musulunci a Jihar Kaduna, Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya ce zai biya wa wani saurayi sadaki domin yi auri budurwarsa wadda iyayenta suka maka shi a kotu.
Alkalin ya kuma buakci matashin da ya je ya yi shawara kan auren budurwar tasa, sannan ya dawo ya sanar da kotu matsayarsa ranar 6 ga watan Satumba, 2022.
- Iyayen Yaran Da Aka Sace A Kano Za Su Kaurace Wa Zaben 2023
- Tsohon Shugaban Kamfanin Jaridar New Nigeria, Tukur Usman, ya rasu
Mahaifiyar budurwar ce ta maka Salele a kotu domin tilasta shi ya auri ’yar tata.
“Unguwarmu daya da shi, kuma kullum sai ya zo zance alhali bai nemi izininmu iyayenta ba.
“Na je na samu mahaifiyarsa na yi mata magana, amma ta ce danta bai isa aure ba.
“Daga nan sai ya daina zuwa, ya koma kiran ta a waya ya ce su hadu a wani wurin.
“Ni kuma ba na so ya lalata min ’ya, shi ya sa na kawo shi kotu.”
Sai dai Salele ya ce shi fa da gaske yana son ’yar tata, amma sai nan da shekaru biyu zai yi aure.
“Ni dalibi ne a jami’a kuma idan an yi aure hankalina zai rabu biyu.
“Kuma ko kudin sadaki ba ni da shi, yanzu ma iyayena ne ke kula da ni”, in ji shi.