Kungiyar Alkalan Kotunan Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, ta roki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rika biya alkalan jihar kudin rawani.
Wannan kira ya fito ne daga Shugaban Kungiyar Alkalan Kotunan Shari’ar Musulunci ta Jihar, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Kano.
Kudin rawani wani bangare ne na alawus-alawus da ake biyan alkalai a Kano.
Alkali Sarki Yola wanda shi ne Alkalin Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a birnin Kano, ya ce alkalai suna da bambanci da sauran ma’aikata lura da yanayin aikinsu, don haka yana da kyau gwamnati ta kula wajen biyan su hakkokinsu.
Ya ce akwai bukatar Gwamnan ya dubi bangarensu kasancewar ya yi umarni a biya su amma har yanzu kudin bai zo hannunsu ba.