Shugaban Kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, ya yi wa fursunoni fiye da 1,000 afuwa albarkacin watan azumi na Ramadana.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da aka fitar daga ofishinsa shugaban, inda ta ce gwamnati za ta yi afuwa ciki har da wasu masu zanga-zanga 70 wadanda mambobin kungiyar Hirak mai fafutukar kafa dimokuradiyya a kasar ne.
- An daure Mubakar Bala shekara 24 kan laifin batanci
- Ramadan: Zulum ya ninka wa ma’aikatan wucin gadi a Borno albashinsu sau uku
Cikin wadanda aka saki akwai Zaki Hannache wanda aka kama a watan Fabrairu saboda tuhumar da aka yi masa na yada labaran kanzon-kurege baya ga tunzura mutane su aikata laifukan ta’addanci.
Kungiyar Hirak ta fara zanga-zanga ne a manyan biranen kasar ta Aljeriya tun a farkon 2019, matakin da ya tilasta wa tsohon shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika, sauka daga mukaminsa.
Hirak ta ci gaba da zanga-zanga bayan da Tebboune ya zama shugaban kasa, sai dai ya yi watsi da matakin kungiyar da ke tuhumarsa da bin sahun tsohuwar gwamnatin kasar.